Litinin 28 Satumba 2026 - 22:27
Darasin Akhlaƙ | Ta Yaya Za Mu Kare Imaninmu Daga “Cututtukan Zuciya”?

Hauza/ Ba ana gwada imani ne kawai a manyan fagen gwagwarmaya ba; wani lokaci son kai da sha’awoyi da suke samun gindin zama a cikin zuciya suna ci gaba da raunana imani a hankali. Wannan magana tana bayyana jihadin yaƙar son rai a matsayin gwagwarmaya ta dindindin domin kare imani da kuma hana mutum zamewa zuwa ga munafunci.

A cewar Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, Shahidin Jagora a cikin littafinsa mai daraja “Mutum Mai Shekaru 250”, ya yi nazari mai zurfi kan hakikanin jihadin yaƙar son rai da kuma haɗarin yin sakaci da cututtukan cikin zuciya. A ƙasa, ga bayanansa dangane da wannan muhimmin batu:

Shahidin Jagoran ya ce: “Lokacin da mutane suka dawo daga yaƙi bayan sun sha wahala mai yawa, Manzon Allah (SAWA) ya ce: ‘Kun dawo daga ƙaramin jihadi, yanzu ku shiga cikin babban jihadi.’

Sai abin ya ba mutane mamaki: ‘Ya Manzon Allah! Menene babban jihadi?’ Mun gudanar da wannan gagarumin jihadi tare da dukkan wahalhalunsa; shin akwai wani jihadi da ya fi wannan girma? Sai ya ce: ‘Eh, jihadin yaƙar son ranku ya fi.’

Idan Alƙur’ani ya ce:

«الّذین فی قلوبهم مرض»

‘Waɗanda suke da cuta a cikin zukatansu’, ba lallai ne dukkan waɗannan su kasance munafukai ba. Tabbas, wasu daga cikin munafukai suna cikin waɗanda suke da cuta a cikin zukatansu, amma ba lallai ne ya zama duk wanda yake cikin «الّذین فی قلوبهم مرض», wato wanda yake da wata cuta a cikin zuciyarsa, ya kasance munafuki ba; wani lokaci mutum mumini ne, amma yana da cuta a cikin zuciyarsa.

To, mene ne ma’anar wannan cuta?

Ma’anarta ita ce raunin ɗabi’a, raunin halayya, bin son rai da sha’awoyi, da kuma son kai iri-iri. Idan ba ka hana waɗannan abubuwa ba, kuma ba ka yaƙe su da kanka ba, za su kwace maka imaninka, su kuma mayar da zuciyarka fanko daga ciki.

Idan suka ƙwace maka imani, zuciyarka za ta zama marar imani, amma zahirinka ya kasance kamar mai imani. A wannan lokacin ne ake kiran irin wannan mutum munafuki.”

Madogara:

Mutum Mai Shekaru 250, shafi na 47.

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha